Yadawa duniya sakamakon nazarta yana da muhimmanci ga rayuwar ka na mai nazarta ko bincike. Sai dai kuma wajejen yada binciken suna da matukar yawa ayanzu, don haka taya zaka iya tantance hanyar da tafi chanchanta ka yada aikin ka?
Bi wannan hanyoyi wajen tabbatar da zaɓin amintacciyar mujalla na wallafa sakamakon binciken ka.
Taya zaka tabbatar cewa jonal da kake tunanin saka aikin ka yayi daidai da risachi naka?

Shin wannan mujallar ta cancanci ka tura mata aikin ka?
Shi jonal din shine mafi daidai da risachi nakan?
- Nazartar da ake wallafa wa na karuwa
- Ko wane sati sabbin jonal fitowa suke
- Labarin mayaudara masu buga jaridar bincike suna kan tashi
- Zai iya zama ƙalubalanci don samun jagora lokacin zabar inda za a buga aikin bincike.

Duba wadannan hanyoyi da aka tsara wajen tabbatar wa kanka wannan jonal din mai aminci ne.
Shin kai ko abokan aikin ka kunsan wannan jonal din?
- Ka taba karanta wani resachi da aka buga a wannan jonal din?
- Shin yana da sauki ne ganin sabbin risachai da aka buga a jonal din?
Zaka iya samun masu wallafa aiki a wannan jonal din cikin sauki ka musu magana?
- Shin anrubuta sunan masu wallafawan ajikin ranar gizo na jonal din?
- Zaka iya samun masu wallafawan ta hanyar talafo, ranar gizo ko aike?
- Shin an baiyana a jikin jonal din hanyoyi da ake bi kafin a buga risachi?
- Shin ana iya ganin risachai da aka buga a wannan jonal din ta hanyoyin dakake amfani dasu?
Shin anrubuta kudin bugawan a fili?
- Shin shafin gidan mujallar ya bayyana abin da za ayi da waɗannan kudade da kuma lokacin da za a caje su?
Ka iya gane kwamiti na edita na jonal din?
- Kaji wani abu akan kwamiti na edita din?
- Su en kwamiti ta edita din sun saka sunan jonal din a ranar gizon su?
Shin masu wallafawan memba ne na ƙwarewar masana’antu da aka sani?
- Suna cikin kwamiti na bin kaidar wallafawa (COPE)?
- Idan jonal din ofin akses ce, tana cikin Directory of Open Access Journals (DOAJ)?
- Idan jonal din ofin akses ce, masu wallafata suna cikin Open Access Scholarly Publishers’ Association (OASPA)?
- Shin jonal din ta bayyana a INASP’s Journals Online platforms (kamar jonal da aka buga a Bangladesh, Nepal, Sri Lanka, Central America da Mongolia) ko kuma a African Journals Online (AJOL, na jonal din Africa)?
- Masu wallafawan memba ne ta wani sanannen kungiya?

Idan duka ko mafi yawan ansoshin ka sun zama ‘eh’ a jerin tambayoyin
Idan duka ko mafi yawan ansoshin ka sun zama ‘eh’ a jerin tambayoyin
- Ka tabbatar kana da yakini wajen cewa jonal da ka zaba amincence ne a idon jama’a.
- Kasan cewa wallafa risachi naka a amincencen jonal zai iya daukaka sunan ka azaman ka na mai bincike
- Yakamata risachi naka yazama me daukaka kuma za a iya samun shi cikin sauki
- Kayi tunanin cewa aikin risachi naka an dubashi kuma anyi editin kafin aka wallafa
- Idan wadannan sun tabbata sai ka tura aikin ka
Many thanks to Muhammad Chutiyami, PhD student at the Institute of Early Childhood at Macquarie University, Australia, for this translation, and to Zainab Yunusa-Kaltungo of the Department of Surgery at the Federal Teaching Hospital, Gombe, Nigeria, for some revisions.